(ABNA24.com) Wata kotu a kasar Lebanon ta fidda sammacin kama mutane 10 yan kasar Libya dangane da bacewar Imam Musa Sadr fiye da shekaru 40 da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a jiya talata ce alkalin kotun binciken bacewar Imam Sadr, mai shari’a Zaher Hamadeh ya fidda sammacin kama mutane, sannan daga cikin wadanda kotun ta bukaci a kama su akwai yayan tsohon shugaban kasar ta Libya marigayi Mu’ammar Kazzafi.
Daga ciki akwai Saiful Islam Gaddafi babban dan tsohon shugaban kasar, sai kuma Abdullahi Sunusi tsohon shugaban ma’aikatar yansandan ciki na kasar, da Ahmad Ramadan tsohon mai bawa Gaddafi shawara kan harkokin tsaro.
Diyar Imam Musa Sadr Haura Al-sadr dai ta yi imanin cewa mahaifinta yana da rai, amma ana tsare das hi ne a wani wuri a cikin kasar ta Libya.
A ranar 31 ga watan Augustan shekara ta 1978 ne Imam Musa Sadr tare da masu rakiyarsa, Sheikh Mohammad Yakub da kuma dan jarida Abbas badruddeen suka ba ce a kasar ta Libya bayan gayyatarsu da tsohon shugaban kasar yaye masu.
/129
24 Yuli 2019 - 09:57
Lambar labari: 964139
Wata kotu a kasar Lebanon ta fidda sammacin kama mutane 10 yan kasar Libya dangane da bacewar Imam Musa Sadr fiye da shekaru 40 da suka gabata.